Kada Ku yi azaba da azabar Allah
Daga Ikramah:
Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi».
أَنَّ عَلِيًّا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ حَرَّقَ قَوْمًا، فَبَلَغَ ابْنَ عَبَّاسٍ فَقَالَ: لَوْ كُنْتُ أَنَا لَمْ أُحَرِّقْهُمْ لِأَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تُعَذِّبُوا بِعَذَابِ اللَّهِ»، وَلَقَتَلْتُهُمْ كَمَا قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ».
Aliyu ibnu Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi ijtihadi sai ya ƙona wasu mutane daga cikin zindiƙai waɗanda suka yi ridda suka bar Musulunci (ya Kona su) da wuta, sai labarin hakan ya kai ga Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, sai ya ƙarfafe shi akan kisan su; sai dai ya yi inkarin ƙona su da wuta. Kuma ya ce: Da ace nine a matsayinsa da ban ƙonasu da wuta ba; domin shi Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu mai yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta, saidai kashesu ya wadatar, inda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk wanda ya yi ridda daga Musulunci ya canja Addinisa zuwa wani Addinin daban to ku kashe shi.
Wajabcin kashe wanda ya yi ridda ya bar Musulunci da ijma'in ma'abota ilimi, hakan da sharuɗɗansa, bamai aikata haka sai shugaba da alƙali.
Faɗinsa: "Wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi" wato: Wanda ya yi ridda daga Musulunci: Hukunci ne gamamme ga maza da mata.
Wanda ya yi ridda ba'a barinsa akan riddarsa, kai za'a kira shi zuwa ga Musulunci, idan bai amsa ba sai a kashe shi.
A cikin wannan hadisin akwai hani akan azabtarwa da wuta, kuma haddodi ba'a zartar da su da wuta.
Falalar Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, da yalwar iliminsa da fahimtarsa da hadisan Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
A cikin wannan akwai ladabin inkari akan wanda ya saɓa.
Sahih Al-Bukhari (4/ 61) (3017).
Kari (14)
عمدة القاري شرح صحيح البخاري.
لبدر الدين العيني (14/ 264).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام.
لعبد الله الفوزان (8/ 364).
توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام.
لعبد الله البسام (6/ 204).
فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام.
لابن عثيمين (5/ 218).
الإفصاح عن معاني الصحاح.
لابن هبيرة (3/ 190).
التوضيح لشرح الجامع الصحيح.
لابن الملقن (18/ 58).
نيل الأوطار.
للشوكاني (7/ 225).
An ambata a cikin littattafai
5 LittattafaiKari (5)
- الإسلام دين كامل«مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ» [2]،
- التسليم للنص الشرعي والمعارضات الفكرية المعاصرة06 التسليم للنص الشرعي - من المبحث الثالث الفصل الرابع حتى الفصل الخامس"من بدل دينه فاقتلوه"
- التسليم للنص الشرعي والمعارضات الفكرية المعاصرة06 التسليم للنص الشرعي - من المبحث الثالث الفصل الرابع حتى الفصل الخامس"لا تعذبوا بعذاب الله"
- حكم المستهزئين بالأنبياء والمرسلين«مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ»[3].
- عقيدة التوحيدعقيدة التوحيد وبيان ما يضادها...«مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ»[61].