Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu".
«يَأْتِي الشَّيْطَانُ أَحَدَكُمْ فَيَقُولُ: مَنْ خَلَقَ كَذَا؟ مَنْ خَلَقَ كَذَا؟ حَتَّى يَقُولَ: مَنْ خَلَقَ رَبَّكَ؟ فَإِذَا بَلَغَهُ فَلْيَسْتَعِذْ بِاللهِ وَلْيَنْتَهِ».
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da maganin abinda ke taso da tambayoyin da Shaidan yake sa wasiwasi akan su ga mumini. Sai Shaidan ya ce: Waye ya halicci abu kaza? waye ya halicci kaza? waye ya halicci sama? kuma waye ya halicci kasa? Sai mumini ya ba shi amsa a Addinance da dabi'ance da hankalce da fadinsa: Allah ne. Saidai Shaidan ba ya tsayawa a wannan iyakar na wasiwasi, kai yana cirata har sai ya ce: Waye ya halicci Ubangijinka? A wannan yayin ne mumini zai ture wadannan wasiwasin da al'amaura uku: Da yin imani da Allah. Da neman tsarin Allah daga Shaidan. Da kuma tsayawa kada ya zarce akan wasuwasin.
...:
Bijirewa daga wasiwasin Shaidan da darshe-darshen sa da rashin tunani a kan su, da fakewa zuwa ga Allah - Madaukakin sarki a cikin tafiyar da su.
Dukkanin abinda yake afkuwa a cikin zuciyar mutum na wasuwasin da ya sabawa shari'a to daga Shaidan ne.
Hani daga tinani a cikin zatin Allah, da kwadaitarwa akan tunani a abubuwan halittarSa da kuma ayoyinSa.
Sahih Al-Bukhari (4/ 123) (3276).
Sahih Muslim (1/ 120) (134).
Kari (5)
إكمال المعلم (1/432).
المفهم (1/345).
فتح الباري (6/ 340).
طرح التثريب (8/163).
بهجة قلوب الأبرار (ص 27).