9 : 91
لَّيۡسَ عَلَى ٱلضُّعَفَآءِ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرۡضَىٰ وَلَا عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ مَا يُنفِقُونَ حَرَجٌ إِذَا نَصَحُواْ لِلَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ مَا عَلَى ٱلۡمُحۡسِنِينَ مِن سَبِيلٖۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.
Explanation & meanings · 1
- Nasĩha ita ce su faɗi maganar ƙwarai; kyautatãwa itace a yi aiki dõmin Allah, ba dõmin neman dũniya ba.