9 : 108
لَا تَقُمۡ فِيهِ أَبَدٗاۚ لَّمَسۡجِدٌ أُسِّسَ عَلَى ٱلتَّقۡوَىٰ مِنۡ أَوَّلِ يَوۡمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِۚ فِيهِ رِجَالٞ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُواْۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُطَّهِّرِينَ
Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa.
Explanation & meanings · 1
- Sunã son tsarkaka ta ɓõye da ta bayyane. Ta ɓõye sananniya ce: ita ce rashin munãfunci, kuma ta bayyane ita ce sunã kãma rũwa a bãyan sun karce kãshinsu da dũtse, kamar yadda ya zo a cikin Hadĩsi. Allah ne Mafi sani.