81 : 24
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ
Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
Explanation & meanings · 1
- Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.