Skip to content
Jerin Surori /

الأنفَال

الأنفَال is chapter 8 of the Quran and has 75 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

75 Ayoyi Lambar Sura 8
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance Mũminai."

Explanation & meanings · 1
  1. Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: "Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa," sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani.

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَإِذَا تُلِيَتۡ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُهُۥ زَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.

ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Watau sunã yin ibãda ta jiki da ta dũkiya wãjiba da nãfila.

أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَمَغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.

كَمَآ أَخۡرَجَكَ رَبُّكَ مِنۢ بَيۡتِكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لَكَٰرِهُونَ

Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.