Skip to content
الأنفَال /

Aya 41

8 : 41

Aya 41 of الأنفَال (8 : 41). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الأنفَال Ayoyi 75
8 : 41

۞ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا غَنِمۡتُم مِّن شَيۡءٖ فَأَنَّ لِلَّهِ خُمُسَهُۥ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا يَوۡمَ ٱلۡفُرۡقَانِ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.

Explanation & meanings · 1
  1. Daga farkon sũrar har zuwa a nan, anã bayãnin cewa ganĩmar Badar bã ta kõwa ba ce fãce Allah da ManzonSa; to, a nan Yanã bayãyin yadda zã a raba dũkiyar, kuma wannan rabon, ya zama sunna ga dukkan dũkiyar ganĩma da Musulmi suka sãmu da yãƙi kõ hari.