Skip to content
البَقَرَة /

Aya 180

2 : 180

Aya 180 of البَقَرَة (2 : 180). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 180

كُتِبَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ إِن تَرَكَ خَيۡرًا ٱلۡوَصِيَّةُ لِلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَ بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma an wajabta, a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.

Explanation & meanings · 1
  1. Bayãnin hukuncin wasiyya: Sunna ta bayyana cewa bãbu wasiyya ga wanda zai yi gãdo, kuma wasiyya bã zã ta shige sulusin dũkiyar tarika ba.