Skip to content
Al'bakara /

Aya 151

2 : 151

Aya 151 of Al'bakara (2 : 151). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Al'bakara Ayoyi 286
Sura · Al'bakara
Hausa · Gummi
2 : 151

كَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِيكُمۡ رَسُولٗا مِّنكُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِنَا وَيُزَكِّيكُمۡ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَيُعَلِّمُكُم مَّا لَمۡ تَكُونُواْ تَعۡلَمُونَ

Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.

Explanation & meanings · 1
  1. Jũyar da alƙibla da yankewa daga dukkan kãfirai da hani daga tsõronsu kuma Allah Ya farkar da Musulmi ga ni'imõmin da Ya yi musu game da aiko Annabi daga gare su, zuwa gare su, a cikinsu, dõmin ya tsarkake su, bayyane da ɓõye, daga dukan ƙurar kãfirci. Wannan ya nũna cewa sai an yi rarrashin mutãne wajen kira zuwa ga addini da kõwace hanya mai yiwuwa. Bãyan haka a yanke wa wanda ya ƙi bin gaskiya bayyane kuma kada a ji tsõronsa. Kuma aka umurce su da fuskanta zuwa ga Allah kawai da tunãwa gare Shi da gõdiya, da nisantar kafirci.