To idan aka ce da kai: Shin yana halatta mu kudurce cewa taurari suna da tasiri bisa abubuwan da suke faruwa(a Duniya) da kuma mutane a cikin janyo alheri da dacewa da kuma samun rayuwa mai kyau ko kuma tunkude wani sharri da abubuwan ki da Bala`o`i ?
السؤال
Tambaya: To idan aka ce da kai: Shin yana halatta mu kudurce cewa taurari suna da tasiri bisa abubuwan da suke faruwa(a Duniya) da kuma mutane a cikin janyo alheri da dacewa da kuma samun rayuwa mai kyau ko kuma tunkude wani sharri da abubuwan ki da Bala`o`i ?
الجواب
Amsa: sai ka ce: Baya halatta a kudurci hakan kwata-kwata saboda babu wani tasiri a garesu cikin yin hakan, kuma babu mai gaskata shugabannin shirme sai masu raunin hankulla da kuma masu bin hauma-hauma, kuma kudurce hakan yana daga shirka saboda fadin sa mai tsira da aminci- a cikin hadisi kudusi: (Hakika Allah yana cewa: Duk wanda ya ce an yimana ruwa da falalar Allah da rahamar sa, to wannan mai yin imani da ni ne mai kafircewa tauraro, wanda kuma ya ce: anyi mana ruwa da nau`i kaza da kaza to wannan mai kfircewa da ni ne, mai yin imani da tauraro ne) Bukhari da muslimu ne suka rawaito. Sai mutanen jahiliyya suke kudurce cewa taurarin nan suna da wani tasiri cikin zuwan ruwan sama