Idan aka ce da kai : Shin ana bibiyar gurabun salihan bayi, da kuma neman albarka da zatin su da gurabun abubuwan da suka bari aiki ne shar`antacce, ko kuma bidi`a ce da bata ?
السؤال
Tambaya/ Idan aka ce da kai : Shin ana bibiyar gurabun salihan bayi, da kuma neman albarka da zatin su da gurabun abubuwan da suka bari aiki ne shar`antacce, ko kuma bidi`a ce da bata ?
الجواب
Amsa: Sai ka ce : Wannan kuduri ne da kuma aiki kirkirarre kagagge saboda sahabban annabin mu Muhammad mai tsira da aminci- sune mafi sanin al`umma kuma mafi falalar ta kuma mafi fahimtar ta kuma mafi kwadayin ta bisa alheri kuma mafi sanin ta da falalar ahalin falalar, amma ba su nemi tabarraki da gurabun Abibakr da umar da usman Aliyu Allah ya kara yadda a garesu, amma kuma basu bibiyi gurabun su ba alhalin sune mafifitan al-umma bayan annabawa, saboda su suna sane da cewar hakan kebantacce ne ga annabi mai tsira da aminci-, kuma hakika umar Allah ya kara yadda a gare shi ya yanke bishiyar da aka yi bai`ati ridwan saboda jin tsoron a rika wuce gona da iri akan ta. Kuma magabata na kwarai sune mafi kwadayin mutane bisa aikin alheri, kuma da ya kasance bibiyar gurabin na su yana da alheri kuma a cikin sa akwai falala to da sun rigaye mu zuwa gare shi