Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

6 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su».
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Dar Al-Kutni ya ruwaito shi a cikin Sunan din sa da waninsa
التصنيف الشرعيالحدود، الأربعون النووية
Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri).
Ingantacce ne Ibnu Khuzaimah da Dar Al-Kutni da Baihaki ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالأذان والإقامة
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi, kuma ya ce: «‌Lallai su basa tsarkakewa».
Ingantacce ne Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi
التصنيف الشرعيالاستنجاء وقضاء الحاجة
«Babu cuta ba cutarwa».
Hasan ne Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin Musnad.
التصنيف الشرعيالقواعد الفقهية والأصولية، الأربعون النووية
"Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".
Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi
التصنيف الشرعيالقواعد الفقهية والأصوليةموضوعات الحديثالظلم، الإحسان إلى الخلقمحاور التعريف بالإسلاممحاسن الأخلاق، عدل الإسلام
"Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba".
Ingantacce ne Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi
التصنيف الشرعيالمسح على الخفين ونحوهما