عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Fon Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Türkmen - Turkmen Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Tace sakamako
Katuna 839
التصنيف الشرعي
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (234)
Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa Madina har sai da muka kasance a wani ruwa a hanya, sai wasu mutane suka yi gaggawar (sallar) La'asar, sai suka yi alwala alhali suna gaggawa, sai muka kai gare su alhali karshen kafafuwanusu suna haske (lam’a) ruwa bai tabasu ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيصفة الوضوء
"Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
التصنيف الشرعيفضل العلم، آداب العالم والمتعلم
Farkon abinda aka fara wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne kyakkyawan mafarki a cikin barci, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya zo masa kwatankwacin hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaici, ya kasance yana kaɗaita a kogon Hira, sai ya yi ibada a cikinsa - shi ne ibada - a wasu ƙididdigaggun darare kafin ya koma gurin iyalansa, kuma yana yin guziri saboda hakan, sannan ya koma ga Nana Khadija, sai ya yi guzuri na kwatankwacinsu (kwanukan), har sai da gaskiya ta zo masa alhali shi yana cikin kogon Hira, sai Mala'ika ya zo masa sai ya ce:
Ka yi karatu, ya ce: «Ni ba mai karatu ba ne» ya ce: «Sai ya kamani sai ya rufeni har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ni ba mai karatu ba ne, sai ya kamani sai ya rufeni karo na biyu har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce:
{Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta Ya halicci mutum daga gudan jini ka yi karatu alhali Ubangijinka shi ne mafi girma}»,
[al-Alaƙ: 1-3].
Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo da su (ayoyin) zuciyarsa tana karkarwa, sai ya shiga wurin Nana Khadija 'yar Kuwailid - Allah Ya yarda da ita -, sai ya ce: «Ki lulluɓeni, ki lulluɓeni» sai suka lulluɓe shi, har sai da razani ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari:
«Haƙiƙa na ji tsoron kaina» sai Nana Khadija ta ce: A'a wallahi, Allah ba zai kunyataka ba har abada, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar ɗawainiya kana bawa wanda ba shi da komai, kana tarbar baƙo, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya, sai Nana Kahadija ta tafi da shi har ta zo da shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, ɗan kawun Nana Khadija. Ya kasance wani mutum ne da ya zama kirista a zamanin jahiliyya, kuma ya kasance yana rubuta harshen Ibraniyanci, yana rubuta Linjila da harshen Ibraniyanci abinda Allah Ya so ya rubuta, kuma ya kasance dattijo ne makaho, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawuna na ! Ka ji magana daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana me ka gani? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta masa labarin da ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Namus ne (Mala'ika) wanda Allah Ya saukarwa (Annabi) Musa shi, kaicona inama dai a ce ni matashi ne a cikin kwanukan da za'a aikoka, inama dai a ce ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Shin yanzu su zasu koreni?», ya ce: Eh, babu wani mutumin da zai zo da irin abinda ka zo da shi sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi.
Sannan Waraƙah kuma bai jima zuwa wani lokaci ba ya rasu, kuma wahayi ya yanke.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيمبعثه صلى الله عليه وسلم
"Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi
التصنيف الشرعيآداب اللباس
Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: "Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
التصنيف الشرعيالأخلاق الحميدة، أعمال القلوب
Aka ce ya Manzon Allah waye mafi azirtar mutane da cetanka a ranar Kiyama? Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Hakika ya Abu Huraira na yi zatan babu daya da zai tambayeni game da wannan hadisin na farko daga kai, saboda abinda na gani na kwadayinka akan hadisi, mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
التصنيف الشرعيالصحابة وفضلهم، فضل العلم، فضائل التوحيد، آداب العالم والمتعلم، توحيد الألوهيةموضوعات الحديثالحث على طلب العلم، الشفاعة، الإخلاصمحاور التعريف بالإسلامالنجاة بالدخول في الإسلام
Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
التصنيف الشرعيحد الردة
"Kowa ne aikin alheri sadaka ne".
Ingantacce ne Bukhari ne ya ruwaito shi daga hadisin Jabir, kuma Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Huzaifa.
التصنيف الشرعيفضائل الأعمال الصالحة، صدقة التطوعموضوعات الحديثحسن الخلق، الإحسان إلى الخلق، صدقة التطوعمحاور التعريف بالإسلاممحاسن الأخلاق