Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike».
Ingantacce ne Imam Ahmad da Tirmithi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa da kuma Hakim ne Suka ruwaito shi
A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Ingantacce ne Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi
"Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku".
Ingantacce ne Hakim da Dabrani ne suka Rawaito shi
"Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma ya tuba zuwa ga Allah, domin cewa duk wanda ya bayyanar mana da aikinsa zamu tsayar da Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka a kansa".
Ingantacce ne Hakim ne ya ruwaito shi da kuma Baihaki
«Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa, idan kuma zai fita to ya yi wa Annabi sallama sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa». (Riwayar) Hakim: «Idan zai fita to ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa».
Hasan ne Ibnu Majah da Hakim ne suka Rawaito shi