Skip to content

Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:

"Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka".

«‌مَنْ ‌جَاءَ ‌مِنْكُمُ ‌الْجُمُعَةَ فَلْيَغْتَسِلْ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ƙarfafa cewa wanda ya yi nufin zuwa sallar Juma'a to an so gareshi ya yi wanka, kamar irin wankansa na janaba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Ƙarfafa wankan Juma'a, kuma cewa shi sunna ne ga mumini ranar Juma'a kuma ya kasance a lokacin tafiya zuwa sallah ya fi.

Kwaɗaitarwa akan tsafta da kyakkyawan ƙanshi yana daga ɗabi'un musulmi da ladubbansa, kuma umarnin yana ƙarfafa a lokacin haɗuwa da mutane da zama da su, musammama dai a Juma'o'i da jam'i.

Magana a cikin hadisin ga wanda Juma'a ta wajaba akansa ne; domin cewa shi ne zai zo Juma’ar.

An so ga wanda zai ke Juma'a ya zama mai tsafta, sai ya yi wanka don wari daga jikinsa ya gushe kuma ya shafa turare, idan ya yi alwala kawai to hakan ya isar masa.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (2/ 81) (1294).

Sahih Muslim (1/ 99) (103).

Kari (6)

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

لعبد الله البسام (ص239).

تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام.

لابن عثيمين (2/ 302).

الإلمام بشرح عمدة الأحكام.

لإسماعيل الأنصاري (1/ 192).