Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
«Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi».
«بَيْنَمَا جِبْرِيلُ قَاعِدٌ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَمِعَ نَقِيضًا مِنْ فَوْقِهِ، فَرَفَعَ رَأْسَهُ، فَقَالَ: هَذَا بَابٌ مِنَ السَّمَاءِ فُتِحَ الْيَوْمَ لَمْ يُفْتَحْ قَطُّ إِلَّا الْيَوْمَ، فَنَزَلَ مِنْهُ مَلَكٌ، فَقَالَ: هَذَا مَلَكٌ نَزَلَ إِلَى الْأَرْضِ لَمْ يَنْزِلْ قَطُّ إِلَّا الْيَوْمَ، فَسَلَّمَ، وَقَالَ: أَبْشِرْ بِنُورَيْنِ أُوتِيتَهُمَا لَمْ يُؤْتَهُمَا نَبِيٌّ قَبْلَكَ: فَاتِحَةُ الْكِتَابِ، وَخَوَاتِيمُ سُورَةِ الْبَقَرَةِ، لَنْ تَقْرَأَ بِحَرْفٍ مِنْهُمَا إِلَّا أُعْطِيتَهُ».
Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya kasance a zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wata ƙara daga sama kamar ƙarar ƙofar da aka buɗe, sai Mala’ika Jibril ya ɗaga kansa da idansa zuwa sama, sannan ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, kuma ba'a taɓa buɗeta ba sai yau ɗin nan, sai wani mala'ika daga cikin mala'iku ya sauko daga gareta zuwa ƙasa, bai taɓa sauka ba kafin nan sai yau, sai mala'ikan ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, kuma ya ce da shi: Ina maka bushara da haske biyu waɗanda aka baka ba'a taɓa bawa wani Annabi kafinka ba; sune: Suratul Fatiha, da kuma ƙarshen ayoyi biyu na Suratul Baƙara. Sannan mala'ikan ya ce: Wani ba zai karanta wani harafi daga garesu ba sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba shi abinda ke cikinsu na alheri da addu'a da kuma abin da yake nema.
Falalar Suratul Fatiha da ƙarshen Suratul Baƙara, da kuma kwaɗaitarwa akan karanta su da aiki da abinda ke cikinsu.
Sama tana da ƙofofi waɗanda umarnin Ubangiji yake sauka daga garesu, kuma ba'a buɗesu sai da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Bayanin girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurin UbangijinSa, inda Ya girmama shi da abinda bai taɓa girmama Annabawan dake gabaninsa ba, sai Ya ba shi waɗannan haske biyun.
Daga tsarin kira zuwa ga Allah yin bushara ta alheri.
Sahih Muslim (1/ 554) (806).
Kari (10)
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (2/ 244).
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (4/ 700).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.
لعلي القاري (4/ 1464).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (2/ 760).
كنوز رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (13/ 122).
An ambata a cikin littattafai
6 Littattafai- ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARIالمنتقى من المتجر الرابح في ثواب العمل الصالح"Yayin da Jibrilu ya ke zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wata ƙara daga sama, don haka ya ɗaga kansa sama, ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai
- Imanin da Allah wanda Ya wajabta shi akan bayinSa daga abinda ya zo a cikin Alkur'ani mai girma da Sunnar Annabta.Daga Abdullahi bn Abbas - Allah ya yarda da shi - ya ce: (Yayin da Jibrilu - amincin Allah ya tabbata a gare shi - zaune tare da Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji wata ƙara daga sama, sai ya ɗaga kansa sama, ya ce:
- Imanin da Allah wanda Ya wajabta shi akan bayinSa daga abinda ya zo a cikin Alkur'ani mai girma da Sunnar Annabta.Daga dan Abbas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Yayin da Jibrilu - amincin Allah ya tabbata a gare shi - yana zaune a wajen annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, ya
Kari (3)
- الخطب المنبريةموسوعة الخطب المنبرية (القسم الثالث)«أَبْشِرْ بِنُورَيْنِ أُوتِيتَهُمَا لَمْ يُؤْتِهِمَا نَبِيٌّ قَبْلَكَ: فَاتِحَةُ الْكِتَابِ، وَخَوَاتِيمُ سُورَةِ الْبَقَرَةِ لَمْ تَقْرَأْ حَرْفًا مِنْهَا إِلَّا أُوتِيتَهُ»
- مجالس تدارس القرآن للمبتدئين (سورة الفاتحة وقصار المفصّل)1(أبشر بنورين أوتيتهما لم يؤتهما نبي قبلك: فاتحة الكتاب، وخواتيم سورة البقرة)([6]).
- مجموعة زاد التفسير (1)التفسير 1بَيْنَما جِبْرِيلُ عليه السلام قاعِدٌ عِنْدَ النبيِّ صلى الله عليه وسلم سَمِعَ نَقِيضا مِنْ فَوقِهِ فَرَفَعَ رأسَهُ، فقال:«هَذا بابٌ مِنَ السَّماءِ فُتِحَ اليَومَ لَمْ يُفْتَحْ قَطُّ إلا اليَومَ، فَنزَلَ مِنهُ مَلَكٌ، فقال: هَذا مَلَكٌ نَزَ