Skip to content
Al'a'raf /

Aya 126

7 : 126

Aya 126 of Al'a'raf (7 : 126). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Al'a'raf Ayoyi 206
Sura · Al'a'raf
Hausa · Gummi
7 : 126

وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنۡ ءَامَنَّا بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتۡنَاۚ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَتَوَفَّنَا مُسۡلِمِينَ

"Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! "

Explanation & meanings · 1
  1. Musulmi shi ne wanda ya sallama kansa ga hukunce-hukuncen Allah waɗanda wani Annabin Allah ya zõ da su, a cikin zãmaninsa. Sabõda haka ma'anar Musulmi shi ne mai sallamãwa ga hukuncin Allah, a kõwane zãmani, tun daga Ãdamu har zuwa Rãnar Ƙiyãma. Sai dai wannan al'umma ta Muhammadu tã keɓanta da sũnan Musulmi, addinin kuma da sũnan Musulunci.