64 : 15
إِنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ
Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina ɗai ne. Kuma Allah, a wurin Sa akwai wani sakamako mai girma.
Explanation & meanings · 1
- Fitina, ita ce duk abin da zai cũci mutum ta hanyar da yake amincewa, cũtar ta dũniya ce kõ ta Lãhira. Cũtar Lãhira ta fi tsanani sabõda girman hasãrar da ke a cikinta.