50 : 14
وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ وَقَوۡمُ تُبَّعٖۚ كُلّٞ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ
Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
Explanation & meanings · 2
- Ma'abũta ƙunci, mutãnen shu'aibu ne na farko. Bãyan an halaka su, sa'an nan ya tafi Madayana.
- Tubba'u, sarkin Himyar ne,a Yemen, yã musulunta amma mutãnensa suka ƙi bin sa ga addini, aka halaka su, shi kuma ya tsĩra. Shĩ ne sarki wanda ya sãɓãwa ƙã'ida; ya musulunta amma mabiyansa ba su musulunta ba.