Skip to content
النِّسَاء /

Aya 129

4 : 129

Aya 129 of النِّسَاء (4 : 129). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 129

وَلَن تَسۡتَطِيعُوٓاْ أَن تَعۡدِلُواْ بَيۡنَ ٱلنِّسَآءِ وَلَوۡ حَرَصۡتُمۡۖ فَلَا تَمِيلُواْ كُلَّ ٱلۡمَيۡلِ فَتَذَرُوهَا كَٱلۡمُعَلَّقَةِۚ وَإِن تُصۡلِحُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Explanation & meanings · 1
  1. Wajen so, bã zã a iya daidaita su ba, sai a daidaita ga kwãna da ciyarwa da wurin kwãna da tufãfi gwargwadon hãlin kõwace.