Skip to content
النِّسَاء /

Aya 119

4 : 119

Aya 119 of النِّسَاء (4 : 119). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 119

وَلَأُضِلَّنَّهُمۡ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمۡ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُبَتِّكُنَّ ءَاذَانَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ وَلَأٓمُرَنَّهُمۡ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلۡقَ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَّخِذِ ٱلشَّيۡطَٰنَ وَلِيّٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِ فَقَدۡ خَسِرَ خُسۡرَانٗا مُّبِينٗا

"Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.

Explanation & meanings · 1
  1. Suna kãtse kunnuwan dabbõbi dõmin su nũna cewa na gumãkansu ne. Sunan mãtã shi ne ga duk abin da ba ya da rai, kamar watã itãtuwa duka mãtã ne. Canza halitta kamar tsãgen fuska da fãƙe haƙõra da karkarar gemu dõmin neman kyau, duka umurnin Shaiɗan ne.