Skip to content
الزُّمَر /

Aya 18

39 : 18

Aya 18 of الزُّمَر (39 : 18). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الزُّمَر Ayoyi 75
39 : 18

ٱلَّذِينَ يَسۡتَمِعُونَ ٱلۡقَوۡلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحۡسَنَهُۥٓۚ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَىٰهُمُ ٱللَّهُۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,

Explanation & meanings · 1
  1. Bãyin Allah na ƙwarai sũ ne waɗanda suke saurãren maganar Allah, sa'an nan su yi aiki da abin da yake mai bayyanannar ma'ana daga gare ta, kuma su bar abin da ba su gãne ma'anarsa ba bãyan sun yi ĩmãni da shi cewa daga Allah yake, kuma su tsarkake Allah daga abin da ba ya sifantuwa da Shi na sũrõrin hãlittarSa.