Skip to content
Aal'Imran /

Aya 75

3 : 75

Aya 75 of Aal'Imran (3 : 75). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Aal'Imran Ayoyi 200
Sura · Aal'Imran
Hausa · Gummi
3 : 75

۞ وَمِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مَنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِقِنطَارٖ يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّنۡ إِن تَأۡمَنۡهُ بِدِينَارٖ لَّا يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيۡكَ إِلَّا مَا دُمۡتَ عَلَيۡهِ قَآئِمٗاۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُواْ لَيۡسَ عَلَيۡنَا فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ سَبِيلٞ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri, zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai." Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.

Explanation & meanings · 2
  1. Ƙinɗar Shi ne ũƙiyya dubũ gõma sha biyu, kuma ũƙiyya ɗaya tanã daidai da dirhami dubũ biyu da ɗari biyar kõ dĩnari dubu.
  2. Bãbu laifi idan mun ci dũkiyarsu: Watau Bayahũde yana ganin cin dũkiyar wanda bã Bayahũde ba irinsa halal ne a gare shi.