Skip to content
البَقَرَة /

Aya 234

2 : 234

Aya 234 of البَقَرَة (2 : 234). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 234

وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَعَشۡرٗاۖ فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.

Explanation & meanings · 1
  1. Bayãnin iddar mutuwar maza; mace ɗiya za ta zauna wata huɗu da kwana gõma. Baiwa mãtar aure tanã a kan rabi. Wadda ke shakkar ciki sai ta zauna sai shakka tã ɗebe. Ana takaba watau mai iddar mutuwa ta nisanci ƙawa kõwace iri ce, sai tã ƙãre idda.