Skip to content
البَقَرَة /

Aya 188

2 : 188

Aya 188 of البَقَرَة (2 : 188). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 188

وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ وَتُدۡلُواْ بِهَآ إِلَى ٱلۡحُكَّامِ لِتَأۡكُلُواْ فَرِيقٗا مِّنۡ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ بِٱلۡإِثۡمِ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kada ku ci dukiyõyinku a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.

Explanation & meanings · 1
  1. Haramun ne cin dũkiyar mutãne da zãlunci. An haɗa wannan ãyã da ta gabãninta, ta azumi, dõmin haɗin hana ci da ya gama su. Sãduwa da mahukunta da dukiya, shi ne rashawa, Allah Yã la'ani mai bãyar da ita da mai karɓarta.