Skip to content
البَقَرَة /

Aya 14

2 : 14

Aya 14 of البَقَرَة (2 : 14). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 14

وَإِذَا لَقُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوۡاْ إِلَىٰ شَيَٰطِينِهِمۡ قَالُوٓاْ إِنَّا مَعَكُمۡ إِنَّمَا نَحۡنُ مُسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."

Explanation & meanings · 1
  1. Kashi na hudu su ne Yahudãwa waɗanda suke sun san gaskiyar Annabcin Muhammadu da Manzancinsa, amma hãsada ta hana su su bi shi, sunã ƙõƙãrin ɓãta abin da ya zo da shi ta hanyar jħfa shibhõhi a ciki, dõmin su kange mutãne daga shigarsa. Sabõda haka aka ce musu shaiɗãnu. Duk wanda ya san gaskiya amma kuma ya yi girman kai daga binta, to, shi ne shaiɗan, daga aljannu kõ daga mutane.