16 : 118
وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا مَا قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُۖ وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
Explanation & meanings · 1
- Gabãnin wancan sũra, kamar a cikin sũratul An'ãm ãyã ta l46. Sabõda haka bã a biyar da Yahũdu a wajen haramcin abin da Allah Ya haramta musu, su kaɗai sabõda zãluncinsu.