Skip to content
يُوسُف /

Aya 7

12 : 7
يُوسُف Ayoyi 111
Sura · يُوسُف
Hausa · Gummi
12 : 7

۞ لَّقَدۡ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخۡوَتِهِۦٓ ءَايَٰتٞ لِّلسَّآئِلِينَ

Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dõmin mãsu tambaya.

Explanation & meanings · 2
  1. Ãyõyi a nan, anã nufin hãlãye waɗanda suka zama darussa na kõyarwa ga mutãne dõmin tarbiyya ga yãra da manya na kõwane matsayi ga rãyuwar ɗan Ãdam.
  2. Yũsufu da ɗan'uwansa shaƙĩƙi, Binyãmĩnu, da sauran gõma. Babbansu ga shekaru, shi ne Raubĩlu, kuma sai Lãwiya. A cikin gidansa aka yi Annabãwa, sai Yahũza kuma shĩ ne shũgabansu a ra'ayi, shĩ ne uban sarãkunansu, sabõda haka sũnansa ya rinjãya a kan ƙabĩlar, aka ce musu Yahũdu.