إمام الحرمين عبد الملك بن عبد الله بن يوسف الجويني
الإسم
Imamul Haramain Abdulmalik bin Abdullah bin Yusuf al-Juwaini
اسم الشهرة
Imamul Haramain
نبذة مختصرة
Abul Ma'ali Abdulmalik bin Abdullah bin Yusuf An-Naisaburi, Imamul Haramaini, masanin Usulul Fiqhu kuma ƙwararren malamin Fiqhun Shafi'iyya. An haife shi a shekara ta 419 H, daga cikin littattafansa akwai "Al-Waraqat" da "Al-Burhan" da sauransu a fannin Usulul Fiqhu, da "Nihayatul Maɗlab" da "Ar-Risalatun Nizamiyyah". As-Sam'ani ya ce: Na karanta a rubutun hannun Abu Ja'afar Muhammad bin Abi Ali cewa na ji Abul Ma'ali yana cewa: (Na karanta dubu hamsin a cikin dubu hamsin, sannan na bar ma'abota Musulunci da Musuluncinsu a cikinta da kuma ilimominsu na zahiri. Na shiga babban kogi mai faɗi kuma na nutse a cikin abin da ma'abota Musulunci suka yi hani a kai, dukkan wannan a kan neman gaskiya. Na kasance ina gudun Taqlidi a zamanin baya, amma yanzu na dawo zuwa ga kalmar gaskiya. Ina horon ku da yin riƙo da addinin mata tsofaffi, idan har Allah bai riske ni da tausasawar jinƙanSa ba in mutu a kan addinin mata tsofaffi, kuma a cika min ƙarshen al'amari na a lokacin barin duniya da kalmar Ikhlasi: 'La ilaha illallah', to bone ya tabbata ga Ibnul Juwaini). Kuma wannan magana ce bayyananniya a kan cewa ya nemi ilimin Kalami abin zargi da kuma ilimin Falsafa, wanda wannan shi ne abin da malaman Musulunci kamar irin su Ash-Shafi'i da sauransu suka yi hani a kai, kuma bayani ne ƙarara kan dawowarsa da tubansa da kuma gargadinsa a kan hakan, kuma wannan shi ne abin da duk wanda ya karanta maganarsa zai fahimta ba tare da wata buƙatar yin tawili ko sharhi ba, ya rasu a shekara ta 478.