أبو يوسف يعقوب بن إبراهيم بن حبيب الفقيه
الإسم
Abu Yusuf Ya'akub ɗan Ibrahim ɗan Habib Faqihi
اسم الشهرة
Abu Yusuf
نبذة مختصرة
Abu Yusuf Yakub ɗan Ibrahim ɗan Habib Al-Ansari Al-Kufi, Alƙali, Mujtahidi, Babban malami, Muhaddisi, Faƙihi ɗan mazhabar Hanafiyya, amintacce a fagen Hadisi. Yana daga cikin ɗaliban Abu Hanifa kuma daga cikin malaman Muhammad ɗan Hasan, kuma shi ne farkon wanda ya yaɗa mazhabar Abu Hanifa. Ya kasance mai faɗin ilimi a kan Tafsiri da Magazi (tarihin yaƙoƙi) da tarihin Larabawa. An haife shi a shekara ta 113, kuma wirdinsa a kowace rana raka'a 200 ne. Az-Zahabi ya ce game da shi: (Abu Yusuf ya kai ƙololuwar shugabancin ilimi yadda babu abin da ya ɗara shi, kuma Ar-Rashid ya kasance yana matuƙar girmama shi), kuma Yahya ɗan Ma'in ya ce: (Ban ga wani a cikin ma'abota ra'ayi wanda ya fi tabbata a Hadisi ba, ko wanda ya fi hadda, ko wanda ya fi ingancin ruwaya fiye da Abu Yusuf), ya rasu a shekara ta 182.