أبو أحمد عبد الله بن عدي بن عبد الله الجرجاني
الإسم
Abu Ahmad Abdullah Bn Adi Bn Abdullah Al-Jurjany
اسم الشهرة
Ibn Adiy
نبذة مختصرة
Abu Ahmad Abdullahi ɗan Adiy ɗan Abdullahi ɗan Muhammad ɗan Mubarak al-Jurjani, Hafizi, Allama, mai tantancewa, kuma an san shi da Ibnu al-Qaɗɗan, Muhaddisi ne daga malaman al-Jarhu wal Ta'adili. An haife shi a shekarar 277, kuma yana ɗaya daga cikin manyan malamai, daga cikin malamansa akwai al-Nasa'i da Ibnu Khuzaimah. Al-Zahabi ya faɗa: (Kuma shi mai adalci ne game da maruwaita gwargwadon ijtihadinsa), kuma shi ne mawallafin littafin "al-Kamil fi Dhu'afa'il Rijal". Hamza ɗan Yusuf ya faɗa: (Na tambayi al-Daraquɗni da ya wallafa littafi a kan raunanan maruwaita, sai ya ce: Ashe ba ka da littafin Ibnu Adiy? Na ce: Ina da shi. Ya ce: Akwai wadatarwa a cikinsa, ba za a ƙara a kansa ba). Ya rasu a shekarar 365.