Skip to content

القاسم بن فيرُّه الشاطبي

الإسم

Al-Ƙasim Bn Firruh al-Shaɗibi

اسم الشهرة

(Asshaɗibi) Wani babban malamin Musulunci da ya fito daga garin Shaɗiba.

نبذة مختصرة

Abu Muhammad al-Ƙasim ɗan Firruh -da kasrar Fa'i da sukunin Ya'un da shaddar Ra'i mai dhamma, ma'anarsa da Larabci: Ƙarfe- ɗan Khalaf ɗan Ahmad al-Ru'aini al-Shaɗibi, Makaho, Masanin Qira'a, Limami, Babban Malami, an haife shi a shekara ta 538, ɗaya daga cikin manyan malaman ƙarni na shida na Hijira. Ya kasance yana da matuƙar hazaƙa, yana da ilimi mai matuƙar zurfi a cikin Qira'o'i da Rasm da Nahawu da Fiqhu da Hadisi, ya wallafa matanai masu amfani a kan hakan, waɗanda yalwar iliminsa, da cikar hankalinsa, da ɗaukakar darajarsa suka bayyana a cikinsu. A lokacin da ya jagoranci Misra matsayinsa ya girmama, sunansa ya bazu, kuma shugabancin karantar da Qira'a ya ƙare a gare shi. Daga cikin wallafe-wallafensa akwai: Nazamin al-Shaɗibiyyah, wato Hirzul Amani wa Wajhut Tahani fil Ƙira'atis Sab'i, da Aƙilatu Atrabil Ƙasa'id fi Asnal Maƙasid wanda yake a kan ilimin Rasm, da Nazimatuz Zuhar fi A'adadi Ayatis Suwar wanda yake a kan ƙirgen ayoyin Mus'hafi da Ilimin Fawasul. Ya rasu a shekara ta 590.

المراجع

Kari (1)
مواقع مختلفة