الحسين بن منصور الحلاج
الإسم
Husaini Bin Mansur Al-Hallaj
اسم الشهرة
(Alhallāj) Mai kaɗa auduga
نبذة مختصرة
Al-Husain ɗan Mansur ɗan Mahmi Al-Hallaj Al-Farisi, Abu Mugith kuma an ce: Abu Abdullah, masanin ilimin kalam kuma masanin falsafa mai da'awar rububiyya. Ya kasance yana bayyana aƙidar Shi'a ga halifofin Abbasiyya da kuma aƙidar Sufanci ga talakawa, alhali a asirce yana da'awar cewa ilahiyya (Ubangiji) ta shiga jikinsa (Hulul), kuma ba ya bayyana hakan sai ga waɗanda ya yarda da su, har sai da asirinsa ya tonu. Ibn Taimiyya ya ce: (A taƙaice dai, babu saɓani a tsakanin al'umma cewa duk wanda ya faɗi aƙidar shigar Allah a cikin ɗan'adam da haɗewarSa da shi, da kuma cewa ɗan'adam zai iya zama abin bauta, ko kuma wannan ɗaya ne daga cikin ababen bauta, to shi kafiri ne wanda jininsa ya halasta, kuma a kan haka ne aka kashe Hallaj). Sannan ya sake cewa: (Kuma abin da ake bayar da labari game da Hallaj na bayyanar karamomi a gare shi a lokacin da ake kashe shi, kamar rubutun da jininsa ya yi a ƙasa cewa: Allah Allah, da nuna farin ciki da kashe shi ko makamancin haka: to dukkanin wannan ƙarya ne, don kuwa Musulmai sun tattara labaran Hallaj a wurare da dama, kamar yadda Thabit ɗan Sinan ya ambata a cikin Akhbarul Khulafa - wanda ya shaida kashe shi - da kamar yadda Isma'il ɗan Ali [Al-Khuɗabi] ya ambata a cikin Tarihin Bagadaza - wanda shi ma ya shaida kashe shi - da kamar yadda Al-Hafiz Abu Bakr Al-Khaɗib ya ambata a cikin tarihinsa, da kamar yadda Al-ƙali Abu Ya'ala ya ambata a cikin Al-Mu'utamad, da kamar yadda Al-Ƙali Abu Bakr ɗan Dhaib da Abu Muhammad ɗan Hazm da wasunsu suka ambata, da kamar yadda Abu Yusuf Al-Ƙazwini da Abul Faraj ɗan Al-Jauzi suka ambata a cikin abin da suka tattara na labaransa. Kuma Shehi Abu Abdurrahman As-Sulami ya ambata a cikin Ɗabaƙat As-Sufiyya cewa mafi yawan mashayaihai sun fitar da shi daga kan Hanyar (Ɗariƙa), kuma Abu Al-Ƙasim Al-Ƙushairi bai ambace shi ba a cikin risalarsa daga cikin mashayaihan da ya lissafa a matsayin mashayaihan Hanyar. Kuma ba mu san wani ɗaya daga cikin jagororin Musulmai da ya ambaci Hallaj da alheri ba, ko daga malamai ko kuma mashayaihai, sai dai wasu mutane sukan yi shiru a kansa; domin ba su san lamarinsa ba). Don haka idan ya halasta a kan Shugaban ɗan'adam (Annabi) ya zama bai san wasu daga cikin munafukai ba alhali suna tare da shi a Madina na tsawon shekaru, saboda faɗin Allah -Ta'ala-: {Kuma daga mutanen Madina akwai waɗanda suka ƙware a kan munafunci, ba ka san su ba, Mu Muka san su, za Mu yi musu azaba sau biyu} [At-Tauba: 101]. To ya fi dacewa a ce halin wata jama'a na munafukai waɗanda babu addinin Musulunci a tattare da su a bayansa - alaihis salatu was salam - zai iya ɓuya ga malaman al'ummarsa, kamar yadda Az-Dhahabi ya faɗa game da Hallaj, da cewa lamarinsa ya shige wa Ibn Khafif da Ibn Aɗa'i da An-Nasrabadi duhu. Kuma yayin da ƙararrakin (da ake kaiwa kan) Hallaj suka yi yawa zuwa ga Al-Muƙtadir Al-Abbasi, ya bayar da umarnin a kama shi, aka ɗaure shi a kurkuku sannan aka gicciye shi kuma aka kashe shi. Ibn An-Nadim ya ruwaito cewa ya kasance mai damfara ne, wanda yake ta'ammali da sufanci, yana da'awar sanin kowane ilimi alhali babu komai a tare da shi daga hakan, kuma yana da ilimin kimiya, sannan ya kasance mai ƙarfin hali a kan sarakuna, mai aikata manyan laifuka, mai son kifar da gwamnatoci, kuma yana da'awar ilahiyya a wurin abokansa, yana faɗin aƙidar shigar Ubangiji a halitta (Hulul), yana bayyana aƙidar Shi'a ga sarakuna da aƙidojin sufanci ga talakawa, sannan a tsakiyar wannan yana da'awar cewa ilahiyya ta shiga jikinsa, Allah Ya ɗaukaka Ya kuma tsarkaka daga abin da yake faɗa. Kuma abin da ake nufi da Hanyar (Ɗariƙa) a cikin maganar Ibn Taimiyya shi ne hanyar masu yawan ibada da masu zuhudu. Ibn Kathir ya ce: (Kuma malamai na Bagadaza sun yi ittifaƙi a kan kafircin Hallaj da zindiƙancinsa, kuma sun yi ijma'i a kan kashe shi da gicciye shi), wato a shekara ta 309.