أمية بن عبد الله أبي الصلت بن أبي ربيعة
الإسم
Umayya ɗan Abdullahi Abi As-Salt ɗan Abi Rabi'a
اسم الشهرة
Umayya bin Abu Salt
نبذة مختصرة
Umayya Bn Abdullahi Abi as-Salt Bn Abi Rabi'a Bn Auf as-Saƙafi, mawaƙin jahiliyya ne mai hikima, daga mutanen Ɗa'if. Ya zo Dimashƙu kafin Musulunci, kuma ya kasance mai masaniya a kan tsofaffin littattafai, kuma shi yana daga cikin waɗanda suka haramtawa kansu giya kuma suka yi watsi da bautar gumaka a jahiliyya, kuma Manzon Allah ya yi hijira zuwa Madina, kuma yaƙin Badar ya auku, sai Umayya ya dawo daga Sham. Yana son Musulunci, sai ya sami labarin kisan mutanen Badar wanda a cikinsu akwai 'ya'yan kawunsa guda biyu, sai ya fasa, kuma ya zauna a Ɗa'if har zuwa lokacin da ya mutu kafiri. Ya rasu a shekara ta 5.