إسماعيل بن إبراهيم الخليل بن آزر
الإسم
(Annabi) Isma'il ɗan (Annabi) Ibrahim badaɗayi ɗan Azara
اسم الشهرة
Isma'il Annabin Allah - aminci ya tabbata a gare shi -
نبذة مختصرة
(Annabi) Isma'il ɗan (Annabi) Ibrahimul Khalil ɗan Azara, daga tsatson Sam ɗan (Annabi) Nuhu, Annabi kuma Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wanda shi ne asalin tsatson Larabawa na uku waɗanda aka sani da Musta'araba, wannan kuwa saboda malaman nasaba sun yi ittifaƙi wajen raba Larabawa zuwa kashi uku: Al-Ba'ida, kamar Adawa da Samudawa da kuma Jurhum ta farko, da Al-Ariba: Larabawan Yaman, daga 'ya'yan Ƙahɗan, da kuma Musta'araba: waɗanda su ne tsatson (Annabi) Isma'il, kuma su ne Larabawan arewacin Tsibirin Larabawa. Haƙiƙa ya taimaka wa mahaifinsa - aminci ya tabbata a gare shi - wajen ginin Ka'aba. Sannan ya yi aure bayan rasuwar mahaifiyarsa, da wata mace daga Jurhum ta biyu (daga Ƙahɗan), inda ta haifa masa 'ya'ya maza goma sha biyu, daga cikinsu akwai (Ƙaidar) kakan Adnan.