أسماء بنت يزيد بن السكن الأنصارية
الإسم
Asma'u ɗiyar Yazid ibnu Sakan Al'ansariyya
اسم الشهرة
Asma'u ɗiyar Yazid - Allah Ya yarda da ita -
نبذة مختصرة
Asma'u ɗiyar Yazid ɗan Sakan ɗan Rafi'u ɗan Imru'ul Ƙais, daga Mutanen Madina, Asadiyya sannan Ashhaliyya, babbar Sahabiya ce, ta shahara da fasaharta kuma an yi mata laƙabi da "Mai jawabin mata". Ta halarci yaƙin Khandaƙ da yaƙin Khaibar, kuma ta fita tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a yaƙin Hudaibiyya, kuma ta yi mubaya'ar Bai'atur Ridwan, kuma a shekara ta sha uku bayan Hijira ta fita zuwa ƙasar Sham inda ta halarci yaƙin Yarmuk a Sham. Ta kasance tana shiga tare da mata wajen shayar da waɗanda suka ji rauni da ɗaure raunukansu, da kuma dukan wanda ya gudu daga fagen daga daga cikin sojojin Musulunci, kuma daga cikin ƙissoshin jaruntakarta shi ne cewa ta tuge gungumen tanti kuma ta shiga dukan kawunan Rumawa da shi har ta kashe mutum tara daga cikin sojojinsu a ranar, kuma a abin da ake ambata ta rawaito hadisai 81. Wasu masana tarihi sun ambace ta a cikin waɗanda suka rasu a shekara ta 69H a lokacin halifancin Abdulmalik ɗan Marwan.