أحمد بن علي بن محمد الكناني العسقلاني
الإسم
Ahmad Bn Ali Bn Muhammad Al-Kinani Al-Asqalani
اسم الشهرة
Ibn Hajar Al-Asqalani
نبذة مختصرة
Abu Al'fadhl Ahmad ɗan Ali ɗan Muhammad ɗan Muhammad ɗan Ali Al'kinani Al'asqalani Hafizi, malami ne, masanin hadisi, masanin fiƙihu, masanin adabi. An haife shi a shekarar 773, ya bayar da kulawa ga adabi da waƙa har ya kai matuƙa a cikinsu, sannan ya fuskanci ilimin hadisi inda ya saurari abubuwa da yawa, kuma ya zamanto Hafizin Musulunci a zamaninsa. Dangane da wallafe-wallafensa kuwa suna da yawa kuma masu amfani, daga cikinsu akwai "Fathul Bari Sharhin Sahih Al'bukhari" da "Al'isabah Fi Tamyizis Sahabah" da "Bulughul Maram Fi Ahadithil Ahkam" da "Tahzibut Tahzib" da kuma taƙaitawar sa "Taƙribut Tahzib", kuma wallafe-wallafensa sun kai ɗari uku. Ya rasu a shekarar 852.