أحمد بن علي المقريزي
الإسم
Ahmad Bn Ali Al-Maƙrizi
اسم الشهرة
(Almaƙreezi) Almaƙirizi
نبذة مختصرة
Abul Abbas Taqiyuddin Ahmad Bn Ali Bn Abdulqadir Bn Muhammad Al'ubaidi Al'maqrizi Al'hanafi sannan Al'shafi'i. An haife shi a shekarar 766, kuma shi masanin tarihi ne ɗan kasar Masar, wanda ya ƙware a fannin adabi, kuma ya ƙware a rubutun zube da na waƙa. Al'hafiz Ibn Hajar ya ce game da shi: "Ya kasance limami ne ƙwararre, mai fasaha, mai ƙwarewa, mahaddaci, mai riko da addini, nagari, mai son Ahlussunnah, yana karkata zuwa ga Hadisi da yin aiki da shi". Kuma ya ce: "Yana da tsarin waka mai kyawun gaske, da rubutun zube mai tsafta, da wallafe-wallafe masu ban sha'awa musamman a tarihin Al'ƙahira; domin haƙiƙa ya raya alamominta, kuma ya bayyana ɓoyayyun abubuwanta, ya sabunta tarihinta, sannan ya kawo tarihin manyan mutanenta". Daga cikin littattafansa akwai: "Al'mawa'iz wal I'itibar bizikril Khiɗaɗ wal Āthār" da "Ighathatul Ummah bi kashfil Ghummah" da "Tajrid Al'tauhid" da "Durar Al'uqud Al'faridah fi Tarajim Al'a'ayan Al'mufidah" da sauransu, ya rasu a shekarar 845.