Skip to content

أحمد بن عبد الرحيم الفاروقي الدهلوي الهندي

الإسم

Ahmad bin Abdurrahim Al-Faruqi Al-Dahlawi Al-Hindi

اسم الشهرة

Ahmad bin Abdurrahim Ad-Dahlawi

نبذة مختصرة

Ahmad ɗan Abdurrahim al-Faruqi al-Dahlawi al-Hindi Abu Abdul'aziz, wanda ake yi wa laƙabi da Shah Waliyyullah, an haife shi a shekarar 1110. Malami ne na Fiqihu a mazhabar Hanafiya kuma daga cikin Malaman Hadisi, daga mutanen Dehli a ƙasar Indiya, ya ziyarci Hijaz a shekarar 1143 - 1145. Mawallafin Fihrisul Faharis ya ce: (Allah ya rayar da Hadisi da Sunnah a Indiya ta dalilinsa da 'ya'yansa da 'ya'yan 'yarsa da ɗalibansu bayan gushewar su, kuma a kan littattafansa da isnadansa ne ake dogara a wancan yanki), kuma mawallafin al-Yani'ul Jani ya ambace shi da suna (Waliyyullah ɗan Abdurrahim). Daga cikin littattafansa akwai "al-Fauzul Kabir fi Usul" wanda ya wallafa shi da harshen Farisanci, kuma an fassara shi bayan rasuwarsa zuwa Larabci da Urdu inda aka yaɗa shi da su, da littafin "Fathul Khabir bima labudda min Hifzihi fi Ilmit Tafsir" da "Hujjatullahi al-Baligha", kuma ya rasu a shekarar 1176, an kuma ce dangane da rasuwarsa: a shekarar 1179.

المراجع

Kari (1)
الأعلام للزركلي(1/149) هدية العارفين(1/177) معجم المؤلفين (1/272) معجم المفسرين (1/43)