أحمد بن أبي دؤاد بن جرير بن مالك الإيادي
الإسم
Ahmad bin Abi Du'ad bin Jarir bin Malik al-Iyadi
اسم الشهرة
Ibn Abi Du'ad
نبذة مختصرة
Abu Abdullahi Ahmad ɗan Faraj ɗan Hariz al-Iyadi al-Basri sannan al-Bagdadi al-Jahami, Alƙali, wanda aka fi sani da Ibnu Abi Du'ad, maƙiyin Sunnah. An haife shi a shekara ta 160, ya kasance mai kira zuwa ga ƙudurcin halittar Alƙur'ani. Yana da karamci da kyauta da ɗimbin ladabi da kyawawan halaye, kuma shi ne ya zama sababin jarrabawa da fitina, kuma ya ce wa Mu'utasim game da Imam Ahmad a cikin fitinar: ("Ya Amirul Muminin, ka kashe shi, shi ɓatacce ne mai ɓatarwa"). Kuma ya tsufa har aka jarrabe shi da cutar shanyewar ɓarin jiki (falaj), kuma Abdul'aziz al-Kinani ya kai masa ziyarar jinya ya ce: ("Ban zo maka a matsayin mai jinya ba, a'a don in gode wa Allah ne a kan yadda Ya ɗaure ka a cikin fatarka"), kuma ya rasu a shekara ta 240.