خارجة بن حذافة بن غانم
الإسم
Kharija ɗan Huzafa ɗan Ganim
اسم الشهرة
Kharija ɗan Huzafa - Allah Ya yarda da shi -
نبذة مختصرة
Kharija ɗan Huzafa ɗan Ganim, daga Bani Ka'abu ɗan Lu'ayyi, babban sahabi ne, daga cikin jarumai. Ya kasance ana lissafa shi daidai da mahaya dawakai dubu. Umar ɗan Khaɗɗab ya aike shi a matsayin ɗauki ga Amru ɗan Al-Asi, sai ya halarci buɗin Misra tare da shi, kuma ya shugabanci 'yan sandansa, kuma ya faru cewa Amru ya yi fama da ciwon ciki a daren da aka ƙulla shirin kisan sa, da kisan Aliyu da Mu'awiyya, sai ya naɗa Kharija a kan yi wa mutane sallah, sai Amru ɗan Bakar wanda aka tura domin kashe Amru ɗan Al-Asi ya kashe shi, kuma makashinsa ya ce a lokacin da ya gane kuskurensa: "Na yi nufin Amru, Allah kuma Ya yi nufin Kharija". Ya rasu a shekara ta 40.