Skip to content

الحجاج بن يوسف بن الحكم الثقفي

الإسم

Alhajjaj bin Yusuf bin Alhakam Atthaƙafi

اسم الشهرة

Alhajjaj Bn Yusuf Atthaƙafi

نبذة مختصرة

Al-Hajjaj ɗan Yusuf at-thaƙafi, an haife shi a shekara ta 40, ya kasance mai yawan zalunci ne, jabari, Nasibi, mai yawan zubar da jini, kuma ya kasance ma'abocin jarumtaka, da ƙarfin hali, da makirci, da kaifin basira, da fasaha, da balaga, da girmama Alƙur'ani, kuma lallai ya yi wa ɗan Zubair ƙawanya a Ka'aba, kuma ya harbe ta da majaniƙ, kuma ya wulaƙanta mutanen Harami biyu kuma ya jinkirtar da salloli. Mulkinsa a kan Iraƙi da Gabas baki ɗaya ya kasance shekaru ashirin ne, kuma yaƙuƙuwan ɗan Ash'as a kansa sun yi tsawo. Az-Zahabi ya ce: (Don haka muna zagin sa kuma ba mu son sa, a'a muna ƙin sa saboda Allah, domin kuwa hakan yana daga cikin mafi ƙarfin igiyoyin Imani, kuma yana da kyawawan ayyuka da suka nutse a cikin tekun zunubansa, kuma al'amarinsa yana ga Allah. Yana da tauhidi a dunƙule, da wasu masu kama da shi daga cikin azzaluman shugabanni da sarakuna), ya rasu a shekara ta 95.

المراجع

Kari (1)
الكامل في التاريخ (4/ 59) البداية والنهاية (12/ 507) الوافي بالوفيات (11/ 237) سمط النجوم العوالي في أنباء الأوائل والتوالي (3/ 293) الأعلام للزركلي(2/ 168)