عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Fon Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Türkmen - Turkmen Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Tace sakamako
Katuna 839
التصنيف الشرعي
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (234)
Na halarci Amr dan Abu Hassan ya tambayi Abdullahi dan Zaid game da alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce a kawo masa kwarya ta ruwa, sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya sanya hannunsa akwaryar, sai ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar, sai ya kuskure baki ya shaka ruwa ya face, kanfata uku, sannan ya shigar da hannunsa sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa sau biyu zuwa gwiwar hannu, sannan ya shigar da hannunsa sai ya shafi kansa, sai ya yi gaba da su ya yi baya sau daya, sannan ya wanke kafafuwansa zuwa idan sawu.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيصفة الوضوءموضوعات الحديثأحكام الوضوء
Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba’a ganin sawunsa, kuma wani daga cikinmu bai sanshi ba, har ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya ɗora tafukansa a kan cinyoyinsa, sai ya ce: Ya Muhammad, ba ni labari game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Sai muka yi mamakinsa, yana tambayarsa yana gasgatashi, ya ce: Ka ba ni labari game da imani, sai ya ce:
"Ka ba da gaskiya da Allah, da mala'ikunsa, da littattafansa, da manzanninsa, da ranar lahira, ka ba da gaskiya da kaddara alherinta da sharrinta". Sai ya ce: ka yi gaskiya, ya ce:
Ka ba ni labari game da kyautayi, ya ce: "Ka bautawa Allah kamar kai kana ganinsa, idan ka kasance ba ka ganinsa, to, shi yana ganinka" Ya ce: ka ba ni labari game da al-ƙiyama, ya ce: Wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sani ba". Ya ce: Ka ba ni labarin alamominta, ya ce: "Kuyanga za ta haifi uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi suna gasar tsawaita gidaje", Ya ce: Sannan ya tafi, sai na zauna ɗan wani lokaci sannan ya ce da ni: "Ya Umar, shin ka san waye mai tambayar?" Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "To, lallai Jibrilu ne ya zo muku don ya sanar da ku addininku".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
التصنيف الشرعيالعقيدة، الأربعون النووية
"Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".
Ingantacce ne Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad.
التصنيف الشرعيالأدعية المأثورة
Mun kasance a wurin Umar, sai ya ce: An hana mu ƙaƙale.
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
التصنيف الشرعيالأخلاق الذميمةموضوعات الحديثالتكلف
"Ka ce : Ya Allah Ka wadatar da ni da halalinKa daga barin haram ɗinKa, kuma Ka wadatani da falalarKa daga wanda ba Kai ba".
Hasan ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
التصنيف الشرعيالأدعية المأثورة
"Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيوجوب الصلاة وفضلها وحكم تاركها، فضل صلاة الجماعة وأحكامها، النفاقموضوعات الحديثصلاة الجماعة
Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa ƙoshi daga abincin alkama a darare uku ajere ba tunda ya zo Madina, har aka karɓi ransa.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالزهد والورع، الهدي النبوي
Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
"Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
"Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah".
Hasan ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
التصنيف الشرعيصفة الصلاة