Skip to content

Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba

Daga Usama Ɗan Zaid Allah Ya yarda da su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.

«مَا تَرَكْتُ بَعْدِي فِتْنَةً أَضَرَّ عَلَى الرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin bai bar jarabawa a bayansa ba mafi cutar da Maza kamar mata ba, idan mace ta kasance cikin iyalansa ne, to, zai dinga kula da ita domin kada ta kaucewa Shari’a, idan kuma wata ce da ban, to, sabo da cuɗanya da kaɗaituwa da ita, da kuma irin barnar da zata biyo bayan haka.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Ya wajaba a kan Musulmi ya kiyayi fitinar mata, ya toshe duk wata hanya da za ta kai ga hakan.

Ya kamata ga Muminai riƙo da Allah da kwaɗayi a wurin sa domin kiyayewa daga fitintinu.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (7/ 8) (5096).

Sahih Muslim (4/ 2097) (2740).

Kari (3)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (373).

فتح الباري لابن حجر (9/ 138).