Skip to content

Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi

Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.

«مَنْ قَرَأَ بِالْآيَتَيْنِ مِنْ آخِرِ سُورَةِ الْبَقَرَةِ فِي لَيْلَةٍ كَفَتَاهُ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin falalar [ayoyin] ƙarshen Baƙara, su ne daga faɗin Allah: (( Manzon ya yi imani….. har zuwa ƙarshen Surah.

Ƙarshen Suratul Baƙara yana tunkuɗewa wanda ya karanta mugun abu da sharri da shaiɗanu, idan ya karanta su da daddare.

Dare yana farawa ne daga faɗuwar rana, yana kuma ƙarewa ne da hudowar alfijir.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (6/ 188) (5008-5009).

Sahih Muslim (1/ 554) (807).

Kari (10)

فتح الباري بشرح صحيح البخاري.

لابن حجر (9/ 56).

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (2/ 240).

تطريز رياض الصالحين.

لفيصل آل مبارك (ص593).

مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.

لملا علي القاري (4/ 1465).

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمصطفى الخِن وغيره (2/ 757).