Skip to content

Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi

Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi

«إِذَا أَنْفَقَ الرَّجُلُ عَلَى أَهْلِهِ يَحْتَسِبُهَا فَهُوَ لَهُ صَدَقَةٌ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bada rabarin cewa idan mutum ya ciyar da iyalinsa waɗanda ciyarwarsu ta wajaba a kansa, kamar matarsa da iyayensa da ‘ya’yansa da sauransu, yana mai neman kusanci zuwaga Allah da hakan, yana neman ladan ciyarwar a wurin Allah, to, Allah zai ba shi ladan sadakarsa.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Samun lada idan aka ciyar da iyali.

Mumini [na gaskiya] yana neman yardar Allah a aikinsa da kuma lada da sakamakon da yake wurin Allah.

Ya kamata a halarto da niyya mai kyau a kowanne aiki, daga cikin hakan akwai lokacin ciyar da iyali.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 20) (55).

Sahih Muslim (2/ 695) (1002).

Kari (8)

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (5/ 334).

شرح رياض الصالحين.

لابن عثيمين (3/ 157).

نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين.

لمصطفى الخن وغيره (1/ 293).

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

سليم الهلالي (1/ 375).