Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro
Daga Usman ɗan Abul Aas al-Saƙafi - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya kai kukan wani ciwo da yake jinsa a cikin jikinsa wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tunda ya musulunta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa:
"Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro".
«ضَعْ يَدَكَ عَلَى الَّذِي تَأَلَّمَ مِنْ جَسَدِكَ، وَقُلْ بِاسْمِ اللهِ ثَلَاثًا، وَقُلْ سَبْعَ مَرَّاتٍ أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ».
Wani ciwo ya kama Uman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya kusa ya halakar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo l ya duba shi, kuma ya sanar da shi wata addu'ar da Allah zai ɗauke masa abinda ya saukar masa na rashin lafiyar; shi ne ya ɗora hannunsa akan wurin da yake jin ciwon, kuma sai ya ce: Bismillah, (Da sunan Allah) sau uku, sannan ya ce sau bakwai: (Ina neman tsari) ina fakewa kuma ina katanguwa (Da Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji)na raɗaɗi a wannan lokacin (kuma nake tsoro) nake jin tsoron faruwarsa a nan gaba na baƙin ciki da tsoro, ko ya wannan cutar ta ci gaba kuma radadinta ya yadu a jiki.
An so mutum ya yi wa kansa tawaida kamar ydda ya zo a cikin hadisin.
Kai kuka - ba tare da kurari ba ko bijirewa - ba ya kore dogaro (ga Allah) da kuma haƙuri.
Addu'a tana daga jumlar aikata sabubba, saboda haka yana kamata a takaitu da lafazzukanta da kuma adadinta.
Wannan addu'ar tana kasancewa ne ga dukkan wani raɗaɗi na gaɓa.
Ɗora hannu akan wurin raɗaɗi a lokacin yin tawaida da wannan addu'ar.
Sahih Muslim (4/ 1728) (2202).
Kari (8)
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (2/ 163).
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (4/ 481).
فيض القدير شرح الجامع الصغير.
لعبدالرؤوف المناوي (1/ 284).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (1/ 689).
An ambata a cikin littattafai
6 Littattafai- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلم«Ina neman tsariN Allah da ikonSa daga sharrin abin da nake ji kuma nake tsoro»[289].
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلمA'ūzu billāhi wa ƙudratihi min sharri mā ajidu wa uhāzir
Kari (4)
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 5«ضَعْ يَدَكَ عَلَىٰ الذي تَألَّمَ مِنْ جَسَدِكَ، وقلْ: بسم الله ثلاثاً، وقُلْ سَبْعَ مرَّاتٍ: أعُوذُ بعزَّة الله وقُدْرتهِ مِنْ شَر ما أجدُ وأحاذِرُ».
- فتاوى المرضىفتاوى المرضى «ضع يدك على الذي تألم من جسدك، وقل: بسم الله، ثلاثًا، وقل سبع مرات: أعوذ بالله وقدرته من شر ما أجد وأُحاذِر»
- مجموعة زاد العقيدة (2)1ضعْ يدَكَ على الذي تألَمُ من جَسَدِك، وقلْ: بسم ﷲ ثلاثًا، وقل سبعَ مراتٍ: «أعوذُ بعزَّةِ ﷲ وقدرتهِ من شرِّ ما أجِدُ وأُحاذرُ»
- مشروع المنهج التعليميمادة التوحيد مستوى 4 «أَعُوذُ بِعِزَّةِ اللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ»