Skip to content

Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:

"Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi".

«مَا نَقَصَتْ صَدَقَةٌ مِنْ مَالٍ، وَمَا زَادَ اللهُ عَبْدًا بِعَفْوٍ إِلَّا عِزًّا، وَمَا تَوَاضَعَ أَحَدٌ لِلهِ إِلَّا رَفَعَهُ اللهُ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa sadaka ba ta rage dukiya, kai! tana tunkuɗe masa illoli, kuma Allah Yana musanyawa mai ita da alheri mai girma, sai ta zama ƙari ba ragi ba. Kuma afuwa tare da iko a kan ramuwa ko kama (mai laifin), ba sa karawa mai yinsu komai sai ƙarfi da buwaya. Kuma wani ba zai ƙanƙan da kai, ya ƙasƙanta ga Allah ba, ba don tsoron wani ba, ba don yaudara (na nuna tausayi) gareshi ba, ba don neman wani abin amfani daga wajensa ba, sai sakamkonsa ya zama ɗaukaka ne da sharafi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Alheri da rabauta (suna ) cikin kamanta shari'a da aikata alheri ko da wasu daga mutane sun yi zaton cewa saɓanin hakan ne.

Manazarta

Sahih Muslim (4/ 2001) (2588).

Kari (8)

توضيح الأحكام من بلوغ المرام.

للبسام (7/ 501).

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (10/ 354).

فتح ذي الجلال والإكرام.

لابن عثيمين (6/ 438).

سبل السلام بشرح بلوغ المرام.

للصنعاني (2/ 692).