Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan bawa ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: bawaNa ya godemin, idan ya ce: {Mai kyauta a duniya mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: BawaNa ya yabeni, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakayya}, Zai ce: BawaNa ya girmamaNi, - wani lokaci kuma ya ce: bawaNa ya fawwala (al'amuransa) gareNi -, idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka kaɗai muke neman taimako}, sai Ya ce: Wannan tsakanina da tsakanin bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan ya ce: {ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar waɗanda Ka yi ni'ima a garesu ba waɗanda Ka yi fushi a kansu ba, ba kuma ɓatattu ba}, zai ce: Wannan ga bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa".
«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: {الْحَمْدُ لِلهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}، قَالَ: مَجَّدَنِي عَبْدِي، -وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي-، فَإِذَا قَالَ: {إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ}، قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ: {اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ، صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلا الضَّالِّينَ}، قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa a hadisi Qudsi: Na raba Surar fatiha a sallah gida biyu tsakanina da tsakanin bawaNa, rabinta nawa ne, rabinta kuma nasane. Rabinta na farko: Godiya ne da yabo da girmama Allah, zan saka masa da mafificin sakamako. Rabinta na biyu: Ƙanƙar da kai ne da addu'a, zan amsa masa, kuma zan ba shi abin da ya roƙa. Idan mai sallah ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah zai ce: BawaNa ya gode min, idan ya ce; {Mai kyauta a duniya Mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah zai ce: BawaNa ya yabeni, sai ya yabeNi ya yi iƙirari da gamewar baiwa ga halittata, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakamako}, Allah zai ce: BawaNa ya girmamaNi, ita ce ɗaukaka mayalwaciya. Idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka ne kaɗai muke neman taimako}, Allah zai ce: Wannan tsakanina ne da tsakanin bawaNa. Ɓangare na farko daga wannan ayar shi ne: {Kai kaɗai muke bautawa} shi ne iƙirari da Allantakar Allah, da kuma amsawa ga yin bauta, da shi ne ɓangaren da yake ga Allah ya kare. Ɓangare na biyu daga ayar shi ga bawa ne: {Gareka ne kaɗai muke neman taimako} neman taimako daga Allah ne, da kuma alƙawarinSa na taimako. Idan ya ce: {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya Hanyar waɗanda Ka yi ni'ima garesu, ba waɗanda Ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba}, Allah zai ce: Wannan ƙanƙar da kai ne da addu'a daga bawaNa, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, haƙiƙa na amsa addu'arsa.
...:
Girman sha'anin Fatiha haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - ya ambaceta (Sallah).
Bayanin kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bawanSa, yayin da ya gode maSa sabo da godewarSa da yabonSa da girmamaShi, kuma Ya yi masa alƙawari zai ba shi abin da ya roƙa.
Wannan surar mai girma ta ƙunshi godiya ga Allah, da ambaton makoma, da roƙon Allah, da tsarkake ibada gareShi, da roƙon shiriya zuwa hanya madaidaiciya, da gargaɗi a kan hanyoyin ƙarya ( bata ) .
Jin wannan hadisin (ji irin na halarto da ma'anarsa) ga mai sallah - idan ya karanta fatiha - zai ƙara masa khushu'insa a sallarsa.
Sahih Muslim (1/ 296) (395).
Kari (4)
إكمال المعلم (2/275).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (2/ 27).
شرح النووي على مسلم (4/103).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (9/ 232) (9/ 253).
An ambata a cikin littattafai
14 LittattafaiKari (14)
- الأربعون في تعظيم قدر الصلاةالأربعون في تعظيم قدر الصلاة «قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِــي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَـــيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَـــأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: ﴿الْحَــمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ﴾، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَـــمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: ﴿
- الصلاة التي علمها النبي ﷺ الصحابة رضي الله عنهمالصلاة التي علمها النبي ﷺ الصحابة رضي الله عنهم«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: (الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ)، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: (الرَّحْمَنِ ا
- الصلاة التي علمها النبي ﷺ الصحابة رضي الله عنهم«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: (الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ)، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: (الرَّحْمَنِ ا
- صلاتنا الخاشعة"قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: ﴿ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴾ [الفاتحة: 2]، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: ﴿
- مجموعة زاد التفسير (1)التفسير 1«قال الله تعالى: قَسَمْتُ الصَّلاةَ بَيني وَبَينَ عَبدي نِصْفَينِ وَلِعَبدي ما سَألَ، فَإِذا قال العبدُ: ﴿الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ﴾ . قال الله تعالى: حَمِدَنِي عَبدي، وإذا قال: ﴿الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ﴾ . قال الله تعالى: أَثنَى
- مجموعة زاد التفسير (1)التفسير 1«فنصفها لعبدي ولعبدي ما سأل»
- محاضرات تعظيم قدر الصلاةمحاضرات في تعظيم قدر الصلاة﴿ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ 2﴾ ، يقول الله تعالى: حمدني عبدي، وإذا قال: ﴿ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ 3﴾ ، يقول الله تعالى: أثنى علي عبدي، وإذا قال: ﴿مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ 4﴾ ، يقول الله تعالى: مجدني عبدي، فإذا قال: ﴿إِيَّاكَ نَعۡبُ
- محاضرات تعظيم قدر الصلاةمحاضرات في تعظيم قدر الصلاة"قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِــي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَـــيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَـــأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: ﴿ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ 2﴾ ، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَـــمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:
- محاضرات تعظيم قدر الصلاةمحاضرات في تعظيم قدر الصلاة" قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: ﴿ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ 2﴾ [الفاتحة: 2]، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ
- محاضرات تعظيم قدر الصلاةمحاضرات في تعظيم قدر الصلاة"هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي "
- محاضرات تعظيم قدر الصلاةمحاضرات في تعظيم قدر الصلاة"هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي "
- مشروع منهاج زادكزادك 1 طالب«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: (ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ)، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: (ٱلرَّحۡمَٰنِ
- من الأحكام الفقهية في الطهارة والصلاة والجنائز«قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: ﴿ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴾ قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمَدَنِي عَبْدِي. وَإِذَا قَالَ: ﴿ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ﴾ قَالَ اللهُ
- نبراس طالب (1)1«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: {الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ(2)}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {الرَّحْمَن