Skip to content

Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:

"Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".

«كَلِمَتَانِ خَفِيفَتَانِ عَلَى اللِّسَانِ، ثَقِيلَتَانِ فِي الْمِيزَانِ، حَبِيبَتَانِ إِلَى الرَّحْمَنِ: سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيمِ، سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba da labari game da kalmomi biyu da mutum zai furta su ba tare da wahala ba, kuma akowane hali, kuma ladansu mai girma ne a ma'auni, kuma Ubangijimmu Al-Rahman - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - Yana sonsu: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi; saboda abin da suka ƙunsa na siffanta Allah da girma da cika, da tsarkakeshi daga tawaya - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.

Ma"anonin Kalmomi

.....:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Mafi girman zikiri shi ne a haɗa tsakanin tsarkakeshi da yabo gareshi a cikinsa.

Bayanin yalwar rahamar Allah ga bayinsa, Yana sakayya da gwaggwaɓan lada a kan aiki kaɗan.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (8/ 86) (6406).

Sahih Muslim (4/ 2072) (2694).

Kari (4)

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (10/ 480).

فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام.

لابن عثيمين (6/ 519).